Dan gwagwarmayar siyasa, Omoyele Sowore, ya zargi jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da taimaka wa wasu ’yan daba wajen kai masa hari tare da tawagarsa a garin Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.

Sowore ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce harin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala wata hira da ya yi a gidan rediyon MIDAS FM 90.5 a ranar Juma’a.

Ya ce mutanen da suka kai harin sun fito ne daga gidan gwamnatin jihar, kuma DSS ta ba su goyon bayan bibiyar motsinsu da kai harin.

Sowore ya kuma zargi jami’an DSS da bibiyarsu da tsangwama tun bayan isarsu Ekiti ranar Alhamis, inda ya ce jami’an sun taɓa yi wa wani manajan wurin cin abinci barazanar kada ya sake ba su damar amfani da wurinsa.

Dan gwagwarmayar ya ce kwamishinan ’yan sandan Jihar Ekiti, Falade Adegoroye Michael, ya ziyarci wurin da aka kai harin tare da ganin raunukan da aka yi musu, sai dai ya nuna rashin jin daɗinsa kan sanarwar rundunar ’yan sandan da ya ce ta bayyana lamarin a matsayin saɓani tsakanin mutane, tare da bayyana raunukan a matsayin ƙanana.

Sowore ya ƙaryata wannan bayani, yana mai cewa ba saɓani aka samu ba, hari aka kai musu. Haka kuma, ya yi zargin cewa kwamishinan ’yan sandan na da hannu a lamarin, duk da cewa bai gabatar da hujjar da ta tabbatar da wannan zargi a saƙonsa ba.

Ya bukaci a ɗauki lamarin da muhimmanci, yana mai cewa bidiyon da ya wallafa ya nuna kwamishinan ’yan sandan bayan ziyarar da ya kai ɗakin gaggawa domin ganin halin da waɗanda suka samu raunukan ke ciki.

Sai dai har yanzu lokacin hada wannan labarin, ba wani martani daga hukumar DSS.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *