Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta bayyana cewa babu wani kuɗi da ake buƙatar masu neman aikin hukumomin tsaro ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida su biya domin gudanar da gwajin ƙwayoyi da ake buƙata a lokacin ɗaukar ma’aikata.

Hukumar ta ce gwajin, wanda aka fi sani da Drug Integrity Test (DIT), ya shafi masu neman aikin Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da kuma Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC).

A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, hukumar ta ce Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta riga ta biya kuɗin gwajin gaba ɗaya domin gudanar da shi ga sabbin ma’aikatan.

NDLEA ta gargaɗi ’yan takara da jami’an hukumomin da abin ya shafa da kada su biya kuɗi ga jami’anta, cibiyoyin gwaji ko ta kowace hanya domin gudanar da wannan gwaji, tana mai cewa babu wani ƙarin kuɗin da ake buƙata.

Hukumar ta kuma umarci ’yan takarar da su shiga shafin gwajin ƙwayoyi na NDLEA ta hanyar mahadar da za a samar a shafukan hukumomin da suke neman aiki, domin yin rajista da cike takardun da ake buƙata kafin gudanar da gwajin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *