Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙaddamar da sabon shirin tallafin jari a makonni masu zuwa, domin taimaka wa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa kusan 250,000 wajen biyan kuɗaɗen gudanar da harkokinsu na wata-wata na tsawon shekara ɗaya.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, bayan da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya karɓi baƙuncin wakilan ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na ƙasar a madadinsa.

Shugaban ya ce gwamnati ta amince da tallafi da shirye-shiryen samar da kuɗaɗen jari naira biliyan 200 a shekarar 2023 domin ƙananan ’yan kasuwa da masana’antun ƙasar.

Ya ƙara da cewa sabon shirin zai taimaka wa ’yan kasuwa wajen biyan buƙatun gaggawa da ci gaba da tafiyar da kasuwancinsu.

A taron, wanda ya samu halartar Ministan Masana’antu na Ƙasa da shugabannin hukumomin SMEDAN, NEXIM, NEPC da ITF, Tinubu ya ce yana son ganin ƙarin ’yan kasuwa sun samu damar yin amfani da kuɗaɗen jari da za su taimaka musu wajen bunƙasa harkokinsu.

Ya kuma bayyana cewa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, ta hannun mai ba shi shawara kan samar da ayyukan yi da ƙananan sana’o’i, na ƙara ƙarfafa hulɗa da masu kasuwanci.

Ya ce tarukan da ake gudanarwa duk bayan watanni uku ƙarƙashin jagorancin Shettima za su ba ’yan kasuwa damar bayyana buƙatunsu, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta cika alkawuran data ɗauka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *