Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana sunayen mutum bakwai da ƙasashe mambobinta suka gabatar domin neman muƙamin Darakta Janar na hukumar, wanda sabon wanda aka zaɓa zai fara riƙewa a ranar 16 ga Agusta, 2027.

 

Cikin waɗanda aka gabatar akwai Dakta Hanan Mohammed Al-Kuwari, Dakta Hanan Balkhy, Dakta Hans Henri P. Kluge, Dakta María P. Neira, Budi Gunadi Sadikin, Dakta Li Song da Dakta Gevorg Tamamyan.

A sanarwar da ta fitar ranar 29 ga Oktoba, 2026, WHO ta ce ’yan takarar za su gana da ƙasashe mambobi da mambobi masu alaƙa da hukumar a ranakun 18 da 19 ga Nuwamba, 2026, a hedikwatarta da ke Geneva, Switzerland.

Za a watsa taron kai tsaye a shafin hukumar cikin harsunanta shida na hukuma.

Hukumar zartarwa ta WHO za ta tantance ’yan takarar tare da rage adadinsu zuwa biyar a zamanta na 160 da za ta gudanar a farkon shekarar 2027.

Daga nan za ta yi hira da waɗanda aka tantance, sannan ta zaɓi mutum uku ko ƙasa da haka domin gabatar da su ga Majalisar Lafiya ta Duniya.

WHO ta ce za a gudanar da taron tattaunawa na biyu da ’yan takarar da hukumar zartarwa ta zaɓa a ranar 15 ga Maris, 2027.

Daga bisani, Majalisar Lafiya ta Duniya za ta naɗa sabon Darakta Janar a zamanta na 80 da za a yi a watan Mayun 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *