Tsohon ministan shari’a na ƙasa kuma ɗan takarar gwamnan jihar Kebbi Karkashin jam’iyyar ADC, Abubakar Malami, ya gode wa al’ummar Jihar Kebbi bisa gagarumin goyon bayan da suka nuna wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, yayin ƙaddamar da kamfen ɗinsa a Birnin Kebbi ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar ranar 6 ga Nuwamba, Malami ya ce yawan mutanen da suka halarci taron da kuma irin goyon bayan da suka nuna sun ƙara masa ƙwarin gwiwar ganin an samu kyakkyawar makoma ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

Malami ya kuma yi Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin barazana, cin zarafi da tashin hankali da suka faru yayin kamfen ɗin.

Ya yi zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan tawagar kamfen, sun lalata kayan aikin kafafen yaɗa labarai, sannan an yi amfani da hayaki mai sa hawaye a wuraren da tawagar baƙi take.

Ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan rushe hedikwatar ƙungiyar Malami Pressure Group da ke kan titin Sani Abacha Bypass a Birnin Kebbi.

Ya ce rashin jituwa ta siyasa bai kamata ya zama dalilin cin zarafi ko hana ’yan adawa gudanar da ayyukansu bisa doka ba, yana mai kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro su mutunta ’yancin faɗin albarkacin baki da gudanar da tarukan lumana.

A cewarsa, Jihar Kebbi na fuskantar matsalolin tsaro, talauci, yunwa da gudun hijirar al’umma sakamakon hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya ce ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali a kai maimakon tsoratar da abokan hamayyar siyasa.

Ya kuma jaddada buƙatar kare manoma, inganta ilimi da kiwon lafiya, ƙarfafa matasa da tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Malami ya buƙaci magoya bayan ADC su ci gaba da zaman lafiya da bin doka, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a siyasa da su mutunta ’yancin jama’a na shiga harkokin siyasa.

Ya ce burinsa shi ne ganin an samar da Kebbi da Najeriya mai tsaro, adalci da damar samun ci gaba ga kowa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *