Taron kwamishinonin yaɗa labarai na jihohin da APC ke mulki ya amince da samar da tsarin haɗa saƙonnin gwamnati tsakanin matakin tarayya da jihohi, domin inganta yadda ake isar da bayanai kan manufofi da ayyukan gwamnati gabanin babban zaɓen 2027.
An cimma matsayar ne a wani taro da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya jagoranta a Abuja ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, wanda ya samu halartar kwamishinonin yaɗa labarai 20 daga jihohin da APC ke mulki.
A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, mahalarta sun amince cewa ya kamata a samar da tsarin saƙonni guda da zai jagoranci jami’an yaɗa labaran gwamnati da masu magana da yawun kamfen, tare da ba su damar daidaita saƙonnin bisa harshe, al’ada da yanayin al’ummomin jihohinsu.
- Malami ya yi Allah-wadai da zargin kai hari kan tawagar ADC a Kebbi
- Najeriya ta nemi UN ta kammala ayyukanta cikin kasafin kudi da wa’adin da aka shata.
Sun kuma jaddada muhimmancin inganta samun bayanai kan ayyukan gwamnatin tarayya da shirye-shiryen tallafi a jihohi, tare da ƙarfafa amfani da kafafen sada zumunta, masu ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai, masu rubutun ra’ayin kansu da sauran masu tasiri a intanet wajen isar da saƙonni.
Sanarwar ta kuma bayyana buƙatar ƙara horas da ministoci, kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati kan yadda za su bayyana ayyukan ma’aikatunsu da amsa tambayoyin jama’a cikin gaskiya da kulawa.
Taron ya kuma bukaci samar da isassun kuɗaɗe domin gudanar da ayyukan yaɗa labarai a jihohi, tare da kauce wa saƙonnin siyasa masu tunzura jama’a da duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali a lokacin zaɓe.
Ministan ya bayyana cewa kundin ayyukan gwamnatin tarayya da aka kammala tattarawa zai kasance ga kwamishinonin ta hanyar takardu da na’ura mai kwakwalwa.
Taron ya kuma amince da ci gaba da ganawa tsakanin ma’aikatar, masu kula da yaɗa saƙonnin kamfen da kwamishinonin jihohi domin ƙarfafa haɗin gwiwa da musayar dabaru gabanin zaɓen 2027.