Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasa ‘yan ƙasa da shekaru 17, Flamingos, murnar kai wa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta shekarar 2026, bayan ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe da suka fafata a ranar Laraba a Morocco.
Tinubu ya bayyana nasarar a matsayin babban abin alfahari da farin ciki ga miliyoyin ’yan Najeriya da ke gida da ƙasashen waje, yana mai cewa kai wa wasan ƙarshe wata babbar nasara ce ga ƙasar.
Shugaban ya kuma yaba wa masu horas da ’yan wasan da sauran waɗanda suka bayar da gudummawa wajen ganin tawagar ta samu nasarar kai wa wannan mataki na gasar.
- Abbas ya bukaci Flamingos su lashe kofin duniya bayan kai wa wasan ƙarshe
- Kwamishinonin APC sun amince da manufofin yaɗa saƙonnin gwamnati gabanin zaɓen 2027
Yayin da Flamingos ke shirin fuskantar Japan a wasan ƙarshe, Tinubu ya buƙaci ’yan wasan su ci gaba da jajircewa, da nuna ƙarfin gwiwa da mayar da hankali, yana mai tabbatar musu da goyon bayan al’ummar Najeriya.
A cikin saƙon nasa, shugaban ya ƙarfafa ’yan wasan su tunkari wasan ƙarshe da irin ƙwazon da ya kai su wannan matsayi, yana mai cewa yana da yakinin za su iya kafa tarihi ta hanyar lashe kofin.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su mara musu baya, domin nasarorinsu na ƙarfafa sauran ’yan mata su cimma burinsu a harkokin wasanni.