Sakataren Yaki na Amurka Pete Hegseth, ya yi gargadi cewa Cuba na iya fadawa rikici da Amurka idan ta nemi kara karfin sojojinta ta hanyar karo makaman yaki na zamani.

Maganganun Hegseth sun zo ne yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke ci gaba da yi wa tsibirin Caribbean barazanar yiwuwar aikawa da sojojin Amurka cikin kasar.

“Zai zama rashin hikima ga gwamnatin Cuba ta yi kokarin samun  damar amfani da irin makaman da za su iya kaiwa wannan sansanin mu ko kuma Amurka,” in ji Hegseth yayin ziyara a sansanin sojin Amurka na tsibirin Guantanamo Bay.

Sakatare Hegseth yace Cuba zata jawo irin rikicin da baa fata, domin babu wata kasa a Duniya da za ta iya yin gogayya da karfin Amurka.”

Maganganunsa sun biyo bayan rahoton da aka fitar a watan Mayu a jaridar Axios, cewar kasar ta sayi sama da jirgi mai sarrafa kansa guda 300 da za a iya amfani da su kan sojojin Amurka.

Cuba na da tazarar kilomita 140, ko mil 90, daga kusurwar kudancin Florida, Jam’iyyar Kwamunis dake takun saka da Amurka ke shugabancin kasar.

Tun bayan fitar da rahoton jaridar Axios, Cuba ta sake jaddada cewa ita ba barazana bace ga kasar Amurka, amma tana da ikon kare kanta daga kowacce irin barazana daga ciki da wajen kasar ta.

Duk da haka, rikici ya tsnanta tsakanin kasashen biyu tun lokacin da Trump ya dawo kan mulki a 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *