Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta umarci kamfanin Air Peace da ya shirya biyan diyya ga fasinjojin da jinkirin jirgin Lagos zuwa Enugu ya shafa.
Matakin ya biyo bayan binciken farko da hukumar ta gudanar, wanda ya gano cewa kamfanin ya aika wa fasinjojin sanarwar da ba daidai ba game da sauya lokacin tashin jirgin.
Jirgin da aka shirya tashinsa da ƙarfe 6:45 na safe ranar Litinin an mayar da lokacin tashinsa zuwa 4:50 na yamma, lamarin da ya sa fasinjoji suka kwashe sa’o’i a filin jirgin Murtala Muhammed.
- NDC na shirin ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen 2027
- Amurka ta ce a shirye take ta gana da Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya
NCAA ta ce kamfanin Air Peace ya kamata ya sanar da fasinjojin tun da wuri cewa an sauya lokacin tashin jirgin, musamman ganin cewa matsalar ta samo asali ne daga tsaiko da ya faru a daren da ya gabata.
Hukumar ta kuma ce Air Peace zai fuskanci matakan ladabtarwa idan bai biya diyya da kulawar da dokokin zirga-zirgar jiragen sama suka tanada ba.
A karkashin dokokin jiragen sama na Najeriya na 2023, kamfanonin jiragen cikin gida dole ne su sanar da fasinjoji dalilin jinkiri cikin mintuna 30 bayan lokacin da jirgi ya kamata ya tashi, tare da tanadar abinci da hanyoyin sadarwa da sauran kulawa gwargwadon tsawon jinkirin.