Ƙungiyar kare haƙƙin tattalin arziki da zamantakewa da tabbatar da riƙon amana, SERAP, ta maka Babban Bankin Najeriya (CBN) a kotu, inda take neman umarnin da zai tilasta wa bankin yin bayanin yadda aka yi da dala miliyan 6.23 da ake zargin an ware domin gudanar da zaɓe, da kuma sama da naira tiriliyan 1.63 na wasu kuɗaɗen gwamnati da Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ya gano akwai matsala a kansu.

An shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2450/2026 ne a ranar Juma’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kamar yadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Matakin ya biyo bayan bayanan da ke cikin kundi na biyu na rahoton binciken kuɗaɗen gwamnati na shekarar 2023, wanda aka wallafa a ranar 7 ga Agustan 2026, daga Janairu zuwa Disamban 2023.

A cewar SERAP, kuɗaɗen da ake magana a kai sun haɗa da dala miliyan 6.23 da aka biya dangane da wata buƙatar kuɗaɗen gudanar da zaɓe da ake zargin an yi ta hanyar zamba, wadda aka jingina ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Sauran kuɗaɗen sun haɗa da sama da naira tiriliyan 1.25 na rancen da CBN ya bai wa gwamnatocin jihohi domin ayyukan tallafi, wanda har yanzu ba a dawo da shi ba, da kuma naira biliyan 116.18 na rancen da aka bai wa bankunan da ke cikin matsalar kuɗi ko waɗanda aka rufe.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa an raba naira biliyan 262.86 a ƙarƙashin shirin Anchor Borrowers, wanda aka ƙaddamar domin tallafa wa manoma.

A cikin ƙarar, SERAP na neman umarnin kotu da zai tilasta wa CBN yin cikakken bayani kan dala miliyan 6.23 da ake zargin an karkatar ko kuma ba a yi cikakken bayanin yadda aka yi amfani da su ba, tare da sama da naira tiriliyan 1.63 na sauran kuɗaɗen gwamnati.

Ƙungiyar ta kuma nemi kotu ta tilasta wa bankin bayyana dalilan bayar da kuɗaɗen, da waɗanda suka amfana da su, da halin da ake ciki na biyan bashin, da matakan da aka ɗauka na dawo da kuɗaɗen da kuma sakamakon binciken cikin gida da CBN ya gudanar kan zargin damfarar kuɗaɗen zaɓe.

Bugu da ƙari, SERAP na neman a tilasta wa bankin bayyana sunayen jami’ai da sauran mutanen da suka amince da bayar da kuɗaɗen, da kuma matakan ladabtarwa ko na gudanarwa da aka ɗauka a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *