Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na Ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya lashe kyautar Gwarzon mai yada labarai na shekara da jaridar Projector Newspaper ta bayar, bisa gudummawar da ya bayar a aikin jarida, sadarwar jama’a da bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya.

An miƙa masa kyautar ne a wani biki da aka gudanar a Merit House, Maitama, Abuja, wanda ya samu halartar manyan mutane daga fannonin siyasa, aikin jarida da hidimar gwamnati.

Ologbondiyan, wanda a yanzu yake riƙe da muƙamin Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar ADC, ya shafe shekaru masu yawa yana taka muhimmiyar rawa a harkokin yaɗa labarai a Najeriya.

A cikin tarihin aikinsa, ya taɓa riƙe muƙamin Editan Siyasa na Ƙungiyar Jaridun THISDAY, da kuma Mataimakin Edita na yau da kullum, inda ya bayar da gudummawa wajen bayar da rahotannin manyan al’amuran siyasa da bunƙasa muhawarar jama’a.

Haka kuma, ya taɓa zama mai ba Sanata David Mark shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a a lokacin da yake Shugaban Majalisar Dattawa.

Ologbondiyan na kuma fitowa a shirye-shiryen rediyo da talabijin domin yin sharhi kan muhimman batutuwan ƙasa.

Da yake karɓar kyautar, Ologbondiyan ya sadaukar da ita ga ’yan jarida a faɗin duniya, bisa gudummawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a, tabbatar da riƙon amana da kuma samar da zaman lafiya a duniya.

Ya ce: “Na sadaukar da wannan kyauta ga maza da mata da ke bayar da rahotannin labarai waɗanda ke taimaka wa duniya ta kasance mafi aminci.”

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci bikin akwai tsohuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, da Sanata Dino Melaye, tare da wasu fitattun mutane daga fannoni daban-daban.

Jaridar Projector Newspaper ta ce kyautar tana karrama mutanen da ayyukansu na ƙwararru da hidimar jama’a suka nuna ƙwarewa, gaskiya da jajircewa a fannoni daban-daban, ciki har da aikin jarida da yaɗa labarai.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *