Masu ruwa da tsaki a taron farko na Majalisar ’Yan Matan Afirka (African Girls Assembly) sun yi kira da a fara zuba jari tun da wuri wajen haɓaka ƙwarewa, ƙarfin gwiwa da damar jagoranci ga ’yan mata, domin magance ƙarancin wakilcin mata a muƙaman shugabanci.
An yi kiran ne a Abuja ranar Asabar, gabanin bikin Ranar ’yar mata ta Duniya da ake gudanarwa duk shekara a ranar 11 ga Oktoba.
Ƙungiyar Educate a Woman Initiative ce ta shirya taron mai taken “Ƙarfafa ’Yan Mata, Shugabannin da ke Sauya Al’umma”, domin ƙarfafa ’yan mata, ba su damar bayyana ra’ayoyinsu da shirya su don jagoranci a Afirka.
- Wike ya zargi Amaechi da almundahana, ya yi barazanar hana shi kamfen a Ribas
- An kama wanda ake zargi da shirya sacewa da kashe manomi a Neja
Mai shirya taron, kuma Daraktar Self Help Africa ta kasa, Joy Aderele, ta ce bai kamata a nemi bai wa ’yan mata kujerun shugabanci kawai ba, sai an tabbatar sun samu ƙwarewar da za ta ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ta ce hakan na buƙatar a fara gina musu ƙarfin gwiwa, ‘yancin yanke shawara da hanyoyin haɗin gwiwa tun suna ƙanana.

Ita ma Love Idoko-Uloko, wadda ta kafa gidauniyar Activate Success International Foundation, ta buƙaci ’yan mata su kawar da tsoro, su bi burinsu tare da amfani da ƙwarewarsu wajen warware matsalolin al’umma.
Ta bayyana cewa shugabanci ba wai kasancewa mutum mai yawan magana ba ne, illa iya kawo sauyi da samar da mafita.
A nata jawabin, Darakta-Janar ta Cibiyar Bunƙasa Mata ta Maryam Babangida, Dakta Adedayo Benjamins-Laniyi, ta buƙaci ’yan matan su gane damar jagoranci da ke tattare da su a gida, makarantu da al’ummominsu.
Ta ce nasarar karatu ya kamata ta kasance tare da ƙarfin hali, gaskiya da riƙon amana, tare da yin kira gare su da kada ƙabila, addini, yanayin iyali ko matsalar kuɗi su zama abin da zai hana su cimma burinsu.

Ellen Hahne, shugabar harkokin siyasa da kasuwanci a Ofishin Jakadancin Sweden da ke Abuja, ta ce ’yan matan da suka halarci taron sun riga sun fara nuna jagoranci ta hanyar ayyukansu a makarantu da al’ummominsu.
Ta kuma jaddada goyon bayan Sweden ga daidaito tsakanin jinsi, tare da ƙarfafa su su yi amfani da muryoyinsu wajen samar da sauyi mai kyau.
Ɗaya daga cikin mahalarta taron, Eleora Aderemi, ta ce bai kamata ’yan mata su bari jinsi ya takaita musu burinsu ko ayyukan da suke son yi ba.

Ita ma Perfecta Silas ta jaddada muhimmancin kare haƙƙin ’yan mata, musamman haƙƙin samun ilimi, tana mai cewa kowace yarinya ta cancanci a saurare ta, a mutunta ta, kuma a ba ta damar koyo da jagoranci.
Taron ya kuma ƙunshi gabatar da waƙoƙin fasaha da tattaunawar ƙwararru kan haƙƙi da bayar da kariya, ƙarƙashin taken “Haƙƙina, Muryata, Makomata”.