Majalisar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC-PCC ta yi kira ga ’yan Najeriya da suka cancanci yin zaɓe da su gaggauta karɓar katunan zaɓensu na din-din-din (PVC), yayin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara aikin raba katunan a faɗin ƙasar.
Majalisar ta tabbatar da cewa za a kare ƙuri’un ’yan Najeriya a babban zaɓen 2027, tana mai gargaɗin cewa ba za a bari wani mutum ko jam’iyyar siyasa ta yi maguɗi ko murƙushe ra’ayin masu zaɓe ba.
- Wike ya zargi Amaechi da almundahana, ya yi barazanar hana shi kamfen a Ribas
- TUC ta umarci mambobinta su yi watsi da yajin aikin NLC a Abuja
- Gwamnatin tarayya ta saki alawus ga manyan ma’aikatan jamio’i
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Juma’a, ADC-PCC ta yi watsi da ikirarin cewa ƙuri’un jama’a ba za su ƙidayu ba, kuma jam’iyyar APC mai mulki za ta rubuta sakamakon zaɓe domin ya amfani ’yan takararta.
ADC, ƙarƙashin ɗan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, za ta tura wakilan jam’iyya zuwa dukkan rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar domin sa ido kan gudanar da zaɓe, kare ƙuri’un jama’a da kuma hana satar nasara.
Ologbondiyan ya buƙaci ’yan Najeriya da kada su karaya, yana mai cewa za su samu damar zaɓen shugabannin da suke so a 2027, kuma babu wanda zai iya hana ra’ayin jama’a idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.