Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗin alawus na musamman ga manyan ma’aikatan jami’o’in tarayya, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi da ke faɗin ƙasar.
Wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar a Abuja, ta bayyana cewa an saki kuɗin alawus ɗin da ake kira CONTA, wato Consolidated Non-Academic Staff Tertiary Institutions Allowance.
Boriowo ta ruwaito Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, yana cewa kuɗin da aka biya na watannin Janairu zuwa Agusta na shekarar 2026, ya nuna ƙudurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kula da walwalar ma’aikata da tabbatar da zaman lafiya a wuraren aiki.
- FCC ta jaddada muhimmancin ingantattun ƙididdiga wajen tabbatar da adalci a wakilcin tarayya
- Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da biyan Naira biliyan 10.32 ga ’yan fansho
- ’Yan sanda sun kama mutane kan jabun lambobin babura da kisan gilla a Neja
Ministan ya ce sakin kuɗin alawus ɗin ya nuna yadda gwamnati ta fahimci muhimmancin jin daɗin ma’aikata, ƙarfafa musu gwiwa da kuma jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka, domin tabbatar da daidaito da ingantaccen aiki a manyan makarantu.
Ya ƙara da cewa biyan kuɗin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na magance korafe-korafen ma’aikata da suka dace, tare da rage katsewar ayyukan karatu a manyan makarantun ƙasar.
Alausa ya bayyana cewa sakin kuɗin ya biyo bayan fara biyan alawus na musamman ga malaman jami’o’i da sauran manyan makarantu, wanda aka fi sani da CATA, a ranar Litinin.
Ministan ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa ma’aikatar za ta ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago da shugabannin cibiyoyin ilimi domin warware sauran matsalolin da ake fuskanta da kuma inganta zaman lafiya da gudanar da ayyukan ilimi yadda ya kamata.
A ƙarshe, ya sake jaddada ƙudurin ma’aikatar na aiwatar da manufofin da ke ba da fifiko ga walwalar ma’aikata, zaman lafiyar cibiyoyin ilimi, bunƙasa ƙwarewar ɗan Adam da inganta sakamakon karatu.