Hukumar Kula da Daidaito a Wakilcin Tarayya ta Najeriya (FCC) ta jaddada muhimmancin ingantattun bayanan ƙididdiga wajen gano gibi a wakilcin al’umma da tabbatar da adalci wajen raba damammaki a hukumomin tarayya.

Hukumar ta bayyana hakan ne lokacin da ta karɓi bakuncin Prince Adeyemi Adeniran, Babban Masanin Ƙididdiga na Najeriya kuma Babban Jami’in Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), wanda ya kai mata ziyarar girmamawa.

FCC ta ce sahihan bayanan ƙididdiga na taimaka wa wajen tantance yadda ake raba damammaki a faɗin ƙasar, da gano wuraren da ake samun ƙarancin wakilci da kuma ƙarfafa sa ido kan hukumomin gwamnatin tarayya bisa hujjoji.

Ta bayyana cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin FCC da NBS na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa ana auna yadda ake aiwatar da manufofin daidaito, da maimakon dogaro da zato kawai.

Hukumar ta ƙara da cewa manufarta ita ce tabbatar da cewa adalci wajen wakilcin jihohi da al’ummomi a naɗe-naɗen tarayya da rabon damammaki ya zama abin da za a iya aunawa, sa ido a kai da kuma tabbatarwa ta hanyar sahihan bayanai.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *