Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 47 da ake zargi da hannu a ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, tare da kwato miyagun ƙwayoyi da makamai masu haɗari a samamen da ta gudanar tsakanin 1 zuwa 7 ga Oktoban 2026.
Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne bisa bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma a sassa daban-daban na jihar, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.
A yankin Panshekara, ’yan sanda sun kama wasu mutane 21 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a samame daban-daban, inda aka kwato ƙwayoyin Pregabalin, Exol, Diazepam da ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.
- An kashe mutum uku a hare-haren da aka kai filayen jiragen saman Saudiyya
- ADC ta ce za ta tattara tare da wallafa sakamakon zaɓe a 2027
Haka kuma, a Kiru an kama wani matashi mai shekaru 22 da zargin safarar miyagun ƙwayoyi, inda aka same shi da kunshe-kunshe 105 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.
A Hotoro kuwa, rundunar ta ce ta kama mutane 13 da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar ’yan daba, wato ’Yan Daba, bayan samun rahoton cewa suna ta addabar jama’a a yankin Hotoro Mahautar Gabas.
Daga hannunsu an kwato kwalabe 216 na wani sinadari da ake kira “Suck and Die”, da kuma takubba, adduna, gatari, wuƙaƙe, sanduna, ƙarafan kaifi da wasu kayayyaki.
Haka kuma, rundunar ta ce jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane sun kama wasu mutane 10 da ake zargi da tada hankalin jama’a a yankin Yan Yashi da Kofar Ruwa a ƙaramar hukumar Dala.
An ce an kwato takubba, adduna, wuƙaƙe, sanduna da ganyen da ake zargin tabar wiwi ne da sauran miyagun ƙwayoyi.
A wani samame kuma, jami’an Special Intervention Squad sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar wayoyin hannu a kusa da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.
Rundunar ta ce an kwato wayoyin Android guda uku da ake zargin an sace, tare da babur mai kafa uku da ake zargin waɗanda ake zargin suke amfani da shi wajen satar wayoyin fasinjoji.
Rundunar ta ce dukkan waɗanda aka kama suna ci gaba da fuskantar bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.
Kwamishinan ’yan sandan ya yaba wa jami’an bisa ƙoƙarinsu, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda bayanan sirri kan ayyukan da ake zargi da aikata laifi.