Jihar Sokoto ta samu mutum 58,573 da suka amfana da shirin koyon ilimin dijital, lamarin da ya sa ta samu lambar yabo ta jagoranci da sauya ayyuka ta hanyar fasaha a Najeriya.
Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) ce ta bayyana hakan a wani taron bita da ta shirya a Abuja, inda aka gabatar da bayanan jihohi da hukumomin da suka shiga shirin.
- Ƙungiyar mata masu goyon bayan Tinubu ta kai ziyara ga Ministan Yaɗa Labarai
- ’Yan sanda sun kama makanikin da ake zargi da satar mota ta Naira miliyan 8 a Kano
Kwamishinan Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Dijital na Sokoto, Bashar Umar Kwabo, ya karɓi lambar yabon a madadin gwamnatin jihar, tare da yaba wa Gwamna Ahmad Aliyu bisa ƙoƙarin bunƙasa fasaha da koyar da ƙwarewar dijital.
Ya kuma yaba wa ma’aikatar da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Sokoto (SICTDA) bisa gudummawarsu, tare da kira gare su da su ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa ilimin dijital da kasuwancin fasaha.
Taron ya kuma tattauna hanyoyin rage gibin ƙwarewar dijital, ciki har da samar da damar amfani da fasaha ga masu buƙata ta musamman, da cimma burin Najeriya na kai ilimin dijital ga kashi 70 cikin 100 na al’umma nan da 2027.