Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kashe Naira biliyan 6.79 wajen tallafin karatu da sauran taimakon ilimi tsakanin Mayun 2023 da Satumbar 2026, tare da taimaka wa ɗaliban da aka kwashe daga ƙasar Sudan sakamakon yaƙi su koma karatu.

Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na jihar, Farfesa Isa Muhammad Maishanu, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan nasarorin ma’aikatar da hukumomin da ke ƙarƙashinta a zamanin gwamnatin Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto.

Maishanu ya ce gwamnatin ta tarar da bashin kuɗin makaranta da rajista da ba a biya ba, wanda ya shafi ɗaliban da ke karatu a manyan makarantu a Najeriya da ƙasashen waje.

Ya ce an kafa kwamitocin tantance basussukan, inda aka biya Naira miliyan 555 domin biyan bashin kuɗin rajistar karatu na 2021/2022 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

Ya ƙara da cewa an tantance tare da biyan basussukan da ake bin jami’o’i 10 a Sudan, Jami’ar Wisconsin da ke Ghana da Jami’ar Integral da ke Indiya.

Haka kuma, gwamnati ta magance matsalolin ɗaliban Sakkwato da aka mayar daga Ukraine zuwa Jami’ar Baze da ke Abuja domin ci gaba da karatunsu.

Kwamishinan ya ce an taimaka wa ɗalibai 72 da aka kwashe daga Sudan domin ci gaba da karatu, yayin da wasu 24 suka kammala karatu ta hanyar yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Jami’ar Sudan International da Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Ya kuma ce an mayar da ɗalibai tara da ke shekarar ƙarshe zuwa Jami’ar Musulunci da ke Uganda domin kammala karatunsu.

Kwamishinan ya bayyana cewa jimillar kuɗin tallafin karatun da aka kashe ya kai Naira 6,791,891,890, wanda ya haɗa da Naira miliyan 945 a shekarar 2023, biliyan 3.08 a 2024, biliyan 2.08 a 2025 da miliyan 605 a 2026, baya ga Naira miliyan 67.2 da aka bayar a matsayin taimako ga ɗaiɗaikun ɗalibai.

Kuɗaɗen sun shafi kuɗin makaranta da rajista, abinci, masauki da sauran buƙatun ilimi da aka amince da su.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *