Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kama mutum biyar da ake zargi da lalata da ƙananan yara mata masu shekaru huɗu, shida, takwas, 10 da 11 a wurare daban-daban na jihar cikin mako guda.

Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar 24 ga Oktoba, 2026, ta ce an samu rahotannin laifukan ne a Garuruwan Yana, Azare, Tilden Fulani, Yelwa da Misau, bayan iyayen yaran sun kai ƙorafi ga ’yan sanda.

Rundunar ta ce a Yana, an kai rahoton lalata da yarinya mai shekara takwas, yayin da a Azare aka kai ƙorafin cewa an yaudari yarinya mai shekara huɗu tare da yi mata barazanar kashe ta idan ta faɗa wa wani. A Tilden Fulani kuma, ana zargin an yaudari yarinya mai shekara 11 da naira 500 kafin aikata laifin.

Haka ma, rundunar ta ce ana zargin wani maƙwabci da lalata da yarinya mai shekara 10 a Yelwa, yayin da a Misau aka kai rahoton cewa an kai yarinya mai shekara shida gona kusa da makabarta aka yi lalata da ita.

Rundunar ta tabbatar da cewa dukkan yaran suna samun kulawar likitoci.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayyana laifukan a matsayin munanan ayyuka, tare da jajantawa iyalan yaran.

Ya ce za a gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar, sannan a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye da su kula da inda ’ya’yansu suke da waɗanda suke tare da su, tare da kai rahoton duk wani cin zarafi ga ’yan sanda cikin gaggawa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *