Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa cutar shan inna na iya sake yaɗuwa a duniya muddin akwai yara da ke ɗauke da cutar, duk da cewa an samu raguwar masu kamuwa da ita da sama da kashi 99 cikin 100 tun shekarar 1988.
Hukumar ta ce cutar, wadda ta fi shafar yara ‘yan ƙasa da shekara biyar, na iya haddasa shanyewar jiki, kuma babu maganin da ke warkar da ita.
Sai dai ana iya kare yara daga cutar ta hanyar yi musu allurar rigakafi.
- Manufofin Gwamnatin Tinubu za su kawo wadata ga ’yan Najeriya —Minista
- Shugaba Tinubu ya ce ba zai sauya salon sauye-sauyen tattalin arziƙinsa ba duk da wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta
A cewar WHO, mutum ɗaya cikin 200 da suka kamu da cutar na iya samun shanyewar jiki, yayin da kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na waɗanda suka samu shanyewar ke mutuwa idan cutar ta shafi tsokokin numfashinsu.
WHO ta bayyana cewa cutar shan inna ta hanyar ƙwayar cutar daji (wild poliovirus) ta ragu daga kimanin mutum 350,000 a ƙasashe sama da 125 a shekarar 1988, zuwa ci gaba da yaɗuwa a Afghanistan da Pakistan, waɗanda har yanzu cutar ke yaɗuwa a cikinsu.
Hukumar ta jaddada cewa allurar rigakafi da sa ido kan yaɗuwar cutar su ne muhimman hanyoyin kawar da ita gaba ɗaya.
Ta kuma ce nasarar shirin rigakafin cutar shan inna ta taimaka wajen hana mutuwar yara kimanin miliyan 1.5 ta hanyar ba su bitamin A yayin gudanar da ayyukan rigakafi.
