Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ƙara yawan mutanen da ake sa ido a kansu sakamakon bullar cutar Ebola da aka tabbatar a ƙasar zuwa 53.
Hakan na zuwa ne yayin da bincike ya faɗaɗa zuwa wani sashen gaggawa da majinyaciyar ta ziyarta a baya.
Darakta-Janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi, inda ya bayar da sabbin bayanai kan aikin gano mutanen da suka yi mu’amala da majinyaciyar.
- Shugaba Tinubu ya ce ba zai sauya salon sauye-sauyen tattalin arziƙinsa ba duk da wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta
- Manufofin Gwamnatin Tinubu za su kawo wadata ga ’yan Najeriya —Minista
Ya ce jami’an lafiya na kuma ƙoƙarin gano mutanen da wataƙila suka yi mu’amala da waɗanda aka riga aka gano, domin tantance girman yiwuwar yaɗuwar cutar da kuma hana ta ci gaba da yaɗuwa.
Adadin wadan da suka kamu ya ƙaruwa daga mutum 44 da gwamnatin tarayya ta sanar da farko, bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya, Abuja, a ranar 20 ga Oktoba.
A baya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa majinyaciyar, wata mata ce da ta dawo daga Uganda a baya-bayan nan, ta fara nuna alamun cutar ne a ranar 7 ga Oktoba, sannan ta nemi kulawar likitoci a ranar 11 ga Oktoba, kafin daga bisani a tabbatar da cewa ta kamu da Ebola.
Idris ya ce hukumar ta gano wasu ƙarin mutane tara da suka yi mu’amala da majinyaciyar kai tsaye, waɗanda ba sa cikin mutum 44 da ke da alaƙa da cibiyar lafiyar.
Ya bayyana cewa ƙarin mutanen sun haɗa da mutum uku daga cikin waɗanda suke zaune tare da majinyaciyar, da kuma mutanen da suka kula da ita a wani sashen gaggawa kafin ta isa cibiyar lafiyar da aka tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar Ebola.
Shugaban NCDC ya bayyana cewa aikin gano waɗanda suka yi mu’amala da majinyaciyar bai tsaya ga mutanen da suka yi hulɗa da ita kai tsaye kawai ba, domin masu binciken na kuma ƙoƙarin gano wasu mutanen da wataƙila suka kamu da cutar ta hanyar hulɗa da waɗanda aka riga aka sanya cikin jerin waɗanda ake sa ido a kansu.