Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Afirka (FAJ) ta jaddada buƙatar amfani da fasahar AI cikin gaskiya, tare da inganta yanayin aikin ’yan jarida domin tabbatar da ingantaccen aikin jarida a nahiyar.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ta gudanar a birnin Addis Ababa na Habasha, a ranakun 24 da 25 ga Oktoba, tare da tallafin UNESCO, Ƙungiyar Kwadago ta Duniya (ILO) da Tarayyar Turai (EU), inda Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) ma ta halarta.

Taron ya tattauna yadda AI za ta taimaka wajen tattara labarai, samar da rahotanni da yaɗa su, da kuma yadda za a iya amfani da ita wajen ƙirƙira da yaɗa bayanan ƙarya.

Mahalarta sun kuma bayyana damuwa kan yadda ake amfani da fasahar wajen maye gurbin ’yan jarida a wuraren aikinsu.

An kuma duba sakamakon binciken FAJ kan yanayin aikin ’yan jarida a Afirka, musamman yadda rashin tabbas kan ayyukan yi da barazanar tsaro ke shafar ikon ’yan jarida na gudanar da rahotannin da ke amfanar jama’a.

Ƙungiyar ta jaddada cewa duk da taimakon da fasaha za ta iya bayarwa, ba za ta maye gurbin ƙwarewar ɗan jarida wajen tantance bayanai, yanke hukunci da ɗaukar alhakin rahoto ba.

Taron ya ƙare da amincewa da wani shirin fafutuka na FAJ domin inganta yanayin aikin ’yan jarida, ingancin aikin jarida da kuma amfani da AI cikin alhaki a faɗin Afirka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *