Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ta ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya bayyana ayyukan more rayuwa da gwamnatinsa ta kammala da kuɗin basussukan da ta karɓa tun hawanta mulki a shekarar 2023.
Jam’iyyar ta bayyana cewa kalaman mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, cewa abin dubawa shi ne abin da ake ginawa ba yawan bashin da ake karɓa ba, cin mutunci ne ga ’yan Najeriya, tana mai cewa ba a ga sakamakon basussukan da gwamnatin ta tara ba.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
- Amnesty ta bukaci a gano inda Omoyele Sowore yake bayan an sace shi a Ekiti
- ADC ta zargi INEC da gazawa wajen shirya zaɓen 2027
- Shekara 20 da rasuwar Sarkin Musulmi Maccido: Abubuwan da za a ci gaba da tunawa da shi
Ya yi zargin cewa aikin da ya fi bayyana a gwamnatin Tinubu shi ne tashar samar da hasken rana da aka girka a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock, domin tabbatar da wutar lantarki a wurin.
Ologbondiyan ya kuma zargi gwamnatin da tallata ayyukan da ba a kammala ba, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun tsaya ne a matakin sanarwa ko tsare-tsare.
Ya ambaci manyan hanyoyin Lagos zuwa Calabar, Sakkwato zuwa Badagry da Trans-Sahara, tare da gyaran layukan rarraba wutar lantarki, a matsayin ayyukan da ya ce ba a ga ci gabansu yadda ya kamata ba. Ya kuma nuna damuwa kan jinkirin aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
ADC-PCC ta yi kira ga ƙasashen da ke bayar da tallafi, abokan hulɗar da cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su ƙara sa ido kan basussukan da Najeriya ke karɓa, tare da buƙatar a tabbatar da gaskiya da yin amfani da kuɗin yadda ya dace.
Ta kuma buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta ƙara bincikar buƙatun karɓar bashi, domin kare tattalin arzikin ƙasar da al’ummomin da za su zo nan gaba.