Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun kashe ’yan ta’adda uku tare da ƙwato bindigar AK-47, alburusai, babur da dabbobi 41 a wasu samame da suka kai a jihohin Kaduna da Kano.

Rundunar ta ce a ranar 29 ga Oktoba, 2026, dakarunta sun fuskanci harin ’yan ta’adda yayin da suke sintiri a kan hanyar Shadow zuwa Old Kuyello, a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Bayan fatattakar maharan, sojojin sun bi sawunsu tare da kashe uku daga cikinsu, sun kuma ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, alburusai uku da babur guda.

Rundunar ta ce babu sojan da ya rasa ransa ko ya ji rauni a lokacin artabun.

A wani samame kuma, ranar 30 ga Oktoba, sojojin sun ƙwato shanu 28 da tumaki 13 a garin Shanono da ke ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wasu da ake zargin ɓarayin dabbobi ne sun gudu suka bar su yayin da suka hango jami’an tsaro.

Rundunar ta ce tana ƙoƙarin miƙa dabbobin ga hukumomin da suka dace, tare da ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci da sauran laifuffuka a yankin Arewa maso Yamma.

Ta kuma buƙaci jama’a su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *