Kamfanin NNPC ya baje kolin shirye-shiryensa na faɗaɗa amfani da iskar gas ɗin CNG, kafa gidajen mai masu tsarin cinikayya, da rarraba silindar gas mai aminci guda miliyan 20 nan da shekarar 2030.

NNPC ya gabatar da waɗannan shirye-shirye ne a bikin baje kolin makamashi na OTL Africa Downstream Energy Week karo na 20, wanda aka gudanar a Legas, inda masana suka tattauna makomar harkokin makamashi a Afirka.

Babban Daraktan Ayyukan Tallace-tallace da Zirga-zirga na NNPC Retail Limited, Baba Shettima Kukawa, ya ce ingantaccen tsarin gudanarwa, kyautata wa abokan ciniki da samar da kayayyaki sun taimaka wajen bunƙasar ayyukan gidajen man kamfanin.

Ya bayyana cewa sama da motoci 150,000 aka sauya su zuwa amfani da CNG cikin shekaru biyu da suka gabata, yayin da sama da tashoshi 90 ke samar da wannan iskar ga masu amfani da ita a kullum a faɗin ƙasar.

A yayin baje kolin, NNPC ta kuma nuna samfurin silindar gas mai aminci da shirin samarwa da rarraba silindar guda miliyan 20 a faɗin Najeriya kafin 2030, domin ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta wajen girki.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *