Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kama wani fasto bisa zargin satar motar Toyota Camry a UTC Plaza, da ke unguwar Garki a Abuja.
Rundunar ta ce ta kama Faston a gidansa ranar 27 ga Oktoba, 2026, bayan gudanar da bincike.
Wanda ake zargin, wanda ya ce shi fasto ne a cocin Salvation Power Bible Ministry da ke jihar Benuwe, ya taimaka wa jami’an ’yan sanda wajen gano tare da kama abokin harkarsa.
- Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike kan kisan Sheikh Yahaya Masussuka
- NNPC zai rarraba silindar gas miliyan 20, da faɗaɗa amfani da CNG a Najeriya nan da 2030
’Yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin, rundunar ’yan sandan jihar Benuwe ta taɓa kama shi kan zargin satar motoci a baya.
Binciken ya kuma danganta waɗanda ake zargin da wata ƙungiyar da ake zargi da satar motoci a jihohi daban-daban da sayar da su.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a harkar, waɗanda har yanzu ba a kama ba.
Ta ce waɗanda aka kama suna hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ta kuma buƙaci jama’a su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.