Masu kutse ta yanar gizo (Hackers) sun sace kudin kirifto da ya kai dalar Amurka biliyan 6.3 daga kamfanin Binance, wanda shi ne babbar kafar musayar kudaden dijital a duniya.

Wannan sata ita ce mafi girma da aka taba samu a tarihi, inda manazarta harkokin tsaron internet suka danganta harin da Koriya ta Arewa.

Sun kuma yi gargadin cewa lamarin na iya girgiza amincewar masu zuba jari da kadarorin dijital.

Bayan sanar da labarin, farashin kudaden kirifto ya fadi a kasuwannin duniya, yayin da Binance ta dakatar da cire kudi daga asusun masu amfani da ita tare da bayyana cewa za ta biya dukkan asarar da aka samu.

Kusan rabin kudaden da aka sace sun samu damar shiga hannun hukumomin da ke samar da kudaden stablecoin, wadanda suka hada da Tether, Circle da World Liberty Financial, kamfanin da ke samun goyon bayan Shugaban Amurka Donald Trump, inda suka gaggauta rufe asusun da kudaden.

Kamfanin binciken harkokin blockchain na TRM Labs ya danganta harin da wani fitaccen bangaren masu kutse na Koriya ta Arewa, wanda ke da alaka da gwamnati.

Kamfanonin TRM Labs da Chainalysis duk sun bayyana cewa suna da kwarin gwiwa matuka cewa Koriya ta Arewa ce ke da alhakin kai harin.

Hukumomin Amurka da Koriya ta Kudu, tare da kwararru kan tsaron yanar gizo, sun bayyana cewa Koriya ta Arewa ta dade tana amfani da kungiyoyin masu kutse da ke da alaka da gwamnatinta wajen leken asiri, satar kudade da samar da kudaden shiga ga kasar.

Sai dai Koriya ta Arewa ta musanta irin wadannan zarge-zarge.

A nata bangaren, Binance ta bayyana cewa kudaden masu amfani da ita suna nan cikin tsaro, kuma tana aiki tare da abokan huldarta domin rufe asusun da wasu daga cikin kudaden da abin ya shafa.

Wannan ya ba maharan damar shiga daya daga cikin tsarin kwamfutocin kamfanin tare dayin cire kudade ba tare da izini ba, kamar yadda Binance ta bayyana.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *