Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Isa Ali Pantami, da ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC, Abdulsalam Gwarzo, su tsaya Takara a zaɓen shekarar 2027.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa amincewar ta dogara ne da sakamakon shari’o’in da har yanzu ake ci gaba da yi a kotuna.

A wani ɓangare kuma, hukumar ta ƙi amincewa da ƙorafin ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun na jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu, wanda ya nemi a sake duba matakin cire sunansa daga cikin jerin sunayen ’yan takarar zaɓe.

Hukumar ta INEC tace ta karɓi ƙorafe-ƙorafe guda 69 daga jam’iyyun siyasa dangane da cire ko rashin sanya sunayen wasu ’yan takara a jerin sunayen waɗanda za su fafata a zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi.

Sai dai hukumar ta ce ta amince da kusan ƙorafe-ƙorafe 36, yayin da ta ƙi amincewa da sauran.

Hukumar ta ƙara da cewa tana jiran cikakkun alkaluma na ƙarshe daga sashen shari’a, wanda ke aiki kan sanarwar da za a fitar dangane da matakan da aka ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *