Sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma sun ce sun samu nasarar dakile harin kwanton ɓaunar ’yan ta’adda a jihohin Zamfara da Sokoto, tare da kuɓutar da wasu makiyaya biyu da kuma kwato dabbobi 520 da aka sace.
A ranar 28 ga Oktoba, 2026, sojojin Sashe na Biyu da ke gudanar da sintiri domin share hanyar Anka zuwa Guruzu a Jihar Zamfara, bayan samun rahotannin hare-haren ’yan ta’adda, sun faɗa cikin kwanton ɓauna da maharan suka shirya a ɓangarorin biyu na hanyar.
Sai dai sojojin sun mayar da martani ta hanyar amfani da ƙarfin wuta, inda suka yi artabu da maharan tare da hallaka da raunata da dama daga cikinsu, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa cikin rudani.
- IMF ya naɗa ɗan China Min Liao a matsayin mataimakin manajan daraktansa
- Atiku ya nemi Tinubu ya riƙa wallafa hotuna da bidiyo daga Makka kullum
Bayan artabun, sojojin sun ci gaba da sintiri a yankin tare da tabbatar da tsaro a hanyar domin bai wa matafiya damar zirga-zirga.
An kuma samu wani soja da ya ji raunin harbin bindiga, wanda aka garzaya da shi asibiti, inda rahoton rundunar ya ce yana cikin kwanciyar hankali.
A wani samame makamancin haka, sojojin sun dakile yunƙurin satar dabbobi da yin garkuwa da makiyaya a ƙauyen Takasaba, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’adda a yankin.
Rundunar ta ce sojojin sun isa wurin cikin gaggawa, suka yi artabu da maharan tare da tilasta musu tserewa, inda suka bar dabbobi 520 da suka sace da kuma makiyaya biyu da suka yi garkuwa da su, waɗanda sojojin suka samu nasarar kuɓutarwa.