Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta riƙa wallafa hotuna da bidiyoyi masu ɗauke da kwanan wata daga Makka a kullum, domin tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu yana gudanar da ibadar Umrah kamar yadda aka sanar.

A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya fitar, Atiku ya yi zargin cewa akwai yiwuwar Tinubu ya yi ɗan gajeren zama a Makka kafin ya wuce Faransa, sabanin sanarwar tafiyarsa domin gudanar da Umrah.

Atiku ya ce bayanan sirri da yake ikirarin yana da su sun nuna cewa Faransa ce ainihin inda shugaban ƙasar zai je.

Ya kuma nemi fadar shugaban ƙasa ta bayyana cikakken jadawalin tafiyar, tare da fayyace ko akwai alaƙa tsakanin ziyarar da lafiyar Tinubu da kuma wani rahoton neman rancen dala biliyan 20 da ya shafi wani abokin hulɗar kasuwanci a Faransa.

Ya ce idan da gaske Tinubu ya tafi Makka domin yin addu’a ga Najeriya, ya kamata a riƙa wallafa hotuna da bidiyoyi na yanzu masu nuna kwanan wata, waɗanda za su tabbatar da kasancewarsa a gaban Ka’aba da gudanar da ibadar Umrah.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin ayyukan da shugaban ƙasar ke gudanarwa a kullum da kuma yadda ake ɗaukar nauyin tafiyar.

Ya ce tafiyar da aka gabatar a matsayin ibadar neman zaman lafiya da ci gaban ƙasa lamari ne da ya shafi jama’a, don haka ya kamata a bayyana bayananta cikin gaskiya da bayyananniyar hanya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku ya ce shi da sauran ’yan Najeriya za su haɗa kai da Tinubu wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *