Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa Makka da ke ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umrah da kuma yin addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya.
Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 28 ga Oktoba, 2026, ta ce ziyarar za ta ba Tinubu damar gudanar da ibada da kuma neman shiriyar Allah kan al’amuran ƙasar.
- Peter Obi ya yi alƙawarin mayar da Arewa cibiyar noma da masana’antu idan ya ci zaɓen 2027
- Atiku ya yi alƙawarin rage haraji ga sabbin kamfanoni, idan ya ci zaben 2027
Yayin zamansa a Makka, shugaban ƙasar zai gudanar da ibadun da suka shafi Umrah, tare da roƙon Allah Ya ba Najeriya da al’ummarta zaman lafiya, kwanciyar hankali, haɗin kai da ci gaba.
Kafin tashinsa daga Abuja, Tinubu zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojin saman Najeriya ta saya domin gudanar da ayyukanta.
Za a gudanar da bikin ƙaddamar da kayan ne a sashen saukar jiragen sama na musamman na fadar shugaban ƙasa da ke filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja.
Sanarwar ta ce ana sa ran shugaban ƙasar zai dawo Najeriya a mako mai zuwa, bayan kammala ibadar Umrah.