Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin samar haraji mai sauƙin ga sabbin kamfanoni a shekarunsu na farko, tare da buɗe musu damar samun kwangilolin gwamnati idan ya zama shugaban ƙasa.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taro na Moonshot by TechCabal da aka gudanar a gidan wasan kwaikwayo na ƙasa da ke Legas, inda ya gana da masu kafa kamfanoni, injiniyoyi da masu ƙirƙire-ƙirƙire a fannin fasaha.

Ya ce yana son samar da manufofin gwamnati da za su taimaka wa kamfanonin fasaha su bunƙasa, yana mai cewa kamfanonin Najeriya sun samu nasarori duk da ƙalubalen manufofin gwamnati da suka fuskanta.

Ɗan takarar ya kuma yi alƙawarin mayar da gwamnati abokiyar cinikin kamfanonin ta hanyar mayar da ayyukan gwamnati, tsarin kasafin kuɗi da sayen kayayyaki da kwangiloli zuwa tsarin dijital.

Atiku ya ce ƙwarewar matasan Najeriya ta nuna irin abin da za su iya cimmawa da kansu, yana mai cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da kamfanonin fasaha zai iya ƙara bunƙasa wannan fanni.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *