Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Dan Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC (ADC-PCC) ya musanta sahihancin wani jadawalin yaƙin neman zaɓe da ke yawo, yana mai cewa takardar ba ta fito daga kwamitin ko ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ba.

Kwamitin ya bayyana cewa jadawalin ba shi da izinin hukuma, don haka bai kamata ’yan Najeriya, da mambobin ADC, da shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauke shi a matsayin sahihin jadawalin ayyukan yaƙin neman zaɓe ba.

A cikin sanarwar, kwamitin ya buƙaci dukkan mambobi da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da takardar, tare da jiran sanarwar hukuma daga ADC-PCC kan ayyukan yaƙin neman zaɓe da jadawalinsu.

Sanarwar, wadda daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ta jaddada cewa kwamitin ne zai fitar da sahihan bayanai game da jadawalin yaƙin neman zaɓen.

Kwamitin ya buƙaci jama’a da su dogara da sanarwar hukuma kawai wajen samun bayanai kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *