Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta miƙa buhuna 69 na busassun ganyen da ake zargin tabar wiwi ne ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da waɗanda abin ya shafa.
Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya miƙa kayan ga hukumar a ranar 27 ga Oktoba, 2026, a wani mataki na haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da laifukan da ke da alaƙa da su.
Rundunar ta ce an gano kayan ne a ranar 27 ga Satumba, 2025, yayin samamen da sashen yaƙi da miyagun ƙwayoyi na rundunar ya gudanar.
- Bincike ya gano cunkoso da tsananin zafi ne suka haddasa mutuwar mutane 33 a hannun NSCDC
- Jihar Jigawa ta tura ɗalibai 65 China karatun digiri na biyu kan noma
kayan a hannun ’yan sanda yayin gudanar da bincike mai zurfi, wanda ya kai ga gano wasu ƙarin buhunan busassun ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.
Bayan kammala binciken da ya dace, rundunar ta miƙa kayan ga NDLEA domin ta ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan shari’a da suka dace, bisa ikon da doka ta ba ta.
Sanusi ya jaddada aniyar rundunar na ƙarfafa haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri da taimakon juna tsakanin hukumomin tsaro domin tarwatsa hanyoyin aikata laifuka.
Ya kuma buƙaci mazauna Abuja su riƙa ba jami’an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.