Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta ce ta kama mutum uku da ake zargi da hannu a ƙungiyar masu garkuwa da mutane, bayan wani samamen haɗin gwiwa da jami’an ’yan sanda da masu gadin daji suka gudanar bisa bayanan sirri.

Rundunar ta ce an fara samun nasarar ne a ranar 24 ga Oktoba, 2026, lokacin da jami’an masu gadin daji suka kama wani mutum a yankin Okolowo da ke Ilorin.

An ce an same shi sanye da kayan mata da hijabi, tare da wata leda mai ɗauke da wasu abubuwa da ake amfani da su a matsayin tsafe-tsafe.

A cewar rundunar, mutumin ya bayyana yayin bincike cewa yana cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane mai mutum tara, wadda ake zargin wani mutum da ake kira Juli ke jagoranta.

’Yan sandan sun ce wanda aka kama ya kuma bayyana cewa ya shiga ayyukan garkuwa da mutane guda uku a Oloru, Alapa da Malete, inda aka karɓi kuɗin fansa.

Bayan ƙarin bincike, jami’an tsaro sun kai samame wani sansanin da ake zargin masu garkuwar ke amfani da shi a ranar 25 ga Oktoba, inda suka kama wasu mutum biyu, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka kama zuwa uku.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ojo Adekimi, ya ce samamen wani mataki ne na ƙoƙarin wargaza ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da kuma inganta tsaro a jihar.

Rundunar ta ce ana ci gaba da binciken waɗanda ake zargin, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *