Kwamitin bincike kan mutuwar fursunoni a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Minna, Jihar Neja, ya bayyana cewa bincikensa bai gano hujjar da ke nuna cewa barkewar cuta ce ta jawo mutuwar mutane 33 da ke tsare a hannun hukumar ba.
Rahoton ya ce bayanan lafiya da na binciken gawarwaki sun nuna cewa mutuwar ta samo asali ne daga matsanancin ƙarancin iska da gazawar numfashi, sakamakon cunkoson ɗakin tsare mutane da rashin isasshen iska.
- Tinubu ba shi da shirin ɗaga Birnin Tarayya daga Abuja zuwa Legas – A4A
- Kwamitin bincike ya ce an gudanar da samamen haƙar ma’adinai a Neja ba tare da cikakken tsari ba
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS, ya bayyana cewa zafi mai tsanani da rashin isasshen ruwan sha sun ƙara jefa fursunonin cikin haɗari.
Ya kuma ce binciken bai gano cewa duka, cututtuka masu yaɗuwa ko cin zarafin da aka yi wa fursunoni ne suka zama musabbabin mutuwar kai tsaye ba.
Rahoton ya kuma yi tsokaci kan zargin wasu waɗanda suka tsira cewa an fesa wani sinadari mai yaɗuwa a cikin ɗakin kafin mutuwar, sai dai kwamitin ya ce bai samu hujjar da za ta tabbatar da zargin ba, don haka ya bayyana shi a matsayin zargin da ba a tabbatar da shi ba.
Duk da haka, kwamitin ya lura cewa an yi binciken gawarwaki uku ne kawai daga cikin mutane 33 da suka mutu, domin an riga an binne sauran gawarwaki 30 kafin isowar tawagar likitoci.