Shugabannin kungiyar A4A

Ƙungiyar Arewa 4 Asiwaju, A4A, da ke fafutukar ganin an sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin zaɓukan 2027, ta buƙaci al’ummar Arewa da su yi watsi da raɗe-raɗin da wasu ke yi na cewa Shugaba Tinubu zai daga Birnin Tarayya daga Abuja zuwa Jihar Legas.

Ƙungiyar ta A4A ta kwatanta raɗe-raɗin a matsayin zance maras gaskiya kuma tushe.

A cewar A4A, abokan hamayya ne suka ƙirƙiri raɗe-raɗin don ɓata wa Shugaba Tinubu suna da kuma janyo mishi baƙin jini a yankin arewa.

Shugaban ƙungiyar A4A reshen Abuja, Muhammad Kabir Shitu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 27 ga watan Oktobar 2026, da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan rantsar da sababbin shugabanni na reshen.

“Wannan zance ne na ɓatanci ba wai na kawo gyara ba. Mutumin da ake zargin wai zai ƙwace Birnin Tarayya amma kuma ya na ayyukan bunƙasa Abuja ta hanyar gina sababbin gine-gine da kuma gina sababbin hanyoyi.”

Da farko, Darakta Janar na ƙungiyar A4A na ƙasa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya buƙaci sabbabin shugabannin da su tallata ayyukan ci gaba da Shugaba Tinubu ya yi don al’umma su sake zaɓensa a 2027 don ya dawo ya ci gaba da ayyukan bunƙasa rayuwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *