Majalisar Yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC-PCC) ta soki buƙatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na neman amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin karɓo ƙarin bashin dala biliyan 20 da fam biliyan ɗaya, tana mai cewa matakin na iya jefa makomar tattalin arzikin Najeriya cikin haɗari.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC-PCC ta ce sabuwar buƙatar bashin na zuwa ne a lokacin da ’yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, ƙarin haraji da kuma cire tallafin man fetur, waɗanda ta ce sun ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga miliyoyin jama’a.
Jam’iyyar ta nuna damuwa kan yadda gwamnatin ke neman ƙarin bashin ƙasashen waje ba tare da bayyana wa ’yan Najeriya yadda aka kashe kuɗaɗen bashin da aka karɓa a baya da kuma kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur ba.
- ’Yan sanda sun kama matashi kan bidiyon da ake zargi da tunzura rikicin addini a Zamfara
- Bincike ya gano cunkoso da tsananin zafi ne suka haddasa mutuwar mutane 33 a hannun NSCDC
Ologbondiyan ya tambayi irin ayyukan more rayuwa da aka aiwatar da kuɗaɗen, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta bayyana amfanin bashin ga jama’a.
ADC-PCC ta yi gargaɗin cewa dogaro da karɓar bashi da ƙara haraji ba tare da inganta samar da kayayyaki, samar da ayyukan yi, ababen more rayuwa da jin daɗin jama’a ba, na iya jefa Najeriya cikin matsalar bashi mai tsanani.
Ta kuma ce nauyin biyan bashin zai iya takaita damar gwamnatocin da za su zo nan gaba wajen tsara manufofin tattalin arziki.
Saboda haka, majalisar ta buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gudanar da cikakken bincike kan sabuwar buƙatar bashin, tare da ƙin amincewa da shi idan gwamnati ba ta gabatar da hujjoji masu gamsarwa kan buƙatarsa, yadda za a biya shi da amfanin da al’umma za su samu ba.
Ta kuma buƙaci Tinubu ya wallafa cikakken bayani kan duk bashin cikin gida da na ƙasashen waje da aka karɓa tun ranar 29 ga Mayu, 2023, tare da bayanin kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur da yadda aka kashe su.
Haka kuma, ADC-PCC ta nemi gwamnati ta bayyana manufar bashin, kuɗin ruwa, wa’adin biya, kuɗaɗen gudanarwa da duk wasu sharuɗɗa ko kadarorin da za a iya jingina.
Ta jaddada cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin nauyin bashin da ake ɗora wa ƙasar da tasirinsa ga makomar tattalin arzikinta, tana mai cewa bai kamata a tilasta wa al’umma biyan bashin da ba a bayyana manufarsa da amfaninsa dalla-dalla ba.