Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kama wani mai shekaru 22, daga Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, bisa zargin hannu a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin yana ɗauke da kalaman da za su iya tunzura rikicin addini.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar a ranar 27 ga Oktoba, 2026, rundunar ta ce bidiyon ya nuna wani matashi sanye da kayan ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS), yana furta kalaman da ake zargin za su iya barazana ga zaman lafiya da zaman tare a tsakanin al’umma.

Sanarwar ta ce rundunar ’yan sanda ta Jihar Zamfara ta tattara bayanan sirri domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin, tare da tuntubar shugabannin JIBWIS na ƙasa da na jiha.

A cewar rundunar, shugabannin ƙungiyar sun nesanta kansu daga abin da ake zargin matashin ya aikata, sannan suka miƙa shi ga ’yan sanda.

Rundunar ta bayyana cewa an fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, inda ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ta dace idan bincike ya samar da isassun hujjojin aikata laifi bisa dokokin ƙasa.

Ta kuma jaddada aniyarta ta kare dukkan ’yan Najeriya ba tare da la’akari da addininsu ba, tare da ɗaukar matakan da doka ta tanada kan duk wani hali da zai iya tunzura ƙiyayyar addini, haddasa tashin hankali ko barazana ga zaman lafiya.

Rundunar ta buƙaci jama’a da su guji sake yaɗa bidiyon ko yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, domin kada su ƙara tayar da hankula ko kawo barazana ga zaman lafiya.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da barin ’yan sanda su kammala binciken.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *