Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce tana binciken hotunan da ake zargin an ƙirƙira da fasahar basirar ɗan’adam (AI) da suka bayyana a rajistar masu zaɓe ta farko da ta wallafa a shafinta na intanet a ranar 26 ga Oktoba, 2026.
A cikin sanarwar da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe na hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar a ranar 27 ga Oktoba, ya ce rajistar da aka wallafa ita ce wadda aka baje a cibiyoyin rajista a faɗin ƙasar daga 9 zuwa 15 ga Oktoba.
Ya ƙara da cewa an gano wasu bayanan rajista masu shakku a lokacin aikin, waɗanda aka ware domin bincike da gyara.
- ADC ta zargi Tinubu da jefa Najeriya cikin haɗarin bauta ta fuskar tattalin arziki saboda sabon bashin waje
- ’Yan sanda sun kama matashi kan bidiyon da ake zargi da tunzura rikicin addini a Zamfara
Hukumar ta bayyana cewa rajistar da aka wallafa a intanet ba ta ƙunshi dukkan gyare-gyaren da ake ci gaba da yi ba, domin rajistar ta farko ce, ba ta ƙarshe da aka tabbatar ba.
Ta ce aikin baje rajistar na ba jama’a damar gano kurakurai da sauran matsaloli kafin kammala tantance bayanan.
INEC ta ce tana kuma binciken yadda hotunan suka shiga rajistar, ciki har da yiwuwar samun kura-kurai na fasaha ko na tsarin aiki, tare da ɗaukar matakan da suka dace bisa sakamakon binciken.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta kammala tantancewa da gyaran bayanai kafin tabbatar da rajistar masu zaɓe ta ƙarshe a ranar 15 ga Disamba, 2026.
Ta kuma gode wa jama’a da suka kai rahoton matsalolin, tana mai cewa za a magance duk wani kuskure da aka tabbatar bisa ƙa’idojin da aka tanada.