Wani kwamitin bincike mai zaman kansa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gano cewa cunkoso da matsanancin zafi ne suka haddasa mutuwar mutane 33 da ke tsare a hannun hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Neja, ciki har da ƙananan yara 14.
A cikin wata sanarwa da ministan ya fitar, ya ce binciken ya nuna cewa mutanen sun rasu ne sakamakon cunkoso mai tsanani, rashin isasshen iska, fuskantar matsanancin zafi na tsawon lokaci da rashin ruwa a jiki.
Ya ƙara da cewa waɗannan matsaloli ne suka haddasa mutuwar, ba barkewar wata cuta ba.
- ADC ta kalubalanci Tinubu ya yi bayani kan zargin cewa wasu ministocinsa sun sayi muƙamansu
- Kwamitin bincike ya bukaci a biya iyalan mamatan da NSCDC ta tsare Naira biliyan 1.4
Tunji-Ojo ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta miƙa cikakken rahoton binciken ga Ofishin Babban Lauyan Tarayya domin ɗaukar matakan shari’a cikin gaggawa.
Ya kuma ce za a dakatar da jami’an da suka yi ƙoƙarin ɓoye bayanai, kawo cikas ga bincike ko lalata hujjoji, tare da tabbatar da cewa sun fuskanci alhakin abin da suka aikata.
Ministan ya ce gwamnatin za ta aiwatar da sauye-sauye a hukumar NSCDC cikin gaggawa, yayin da tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu da mutanen da suka tsira ke cikin manyan abubuwan da za a ba fifiko.
Ya jaddada cewa gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Ministan ya kuma yaba wa mambobin kwamitin ƙarƙashin jagorancin Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS, tare da Farfesa Isa Hayatu Chiroma, SAN, tsohon Darakta-Janar na Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya, wanda ya kasance sakataren kwamitin.
Sauran mambobin sun haɗa da tsohon Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda Hosea Hassan Karma, Farfesa Olayinka Buhari, wakilan Majalisar Masarautar Minna da gwamnatin Jihar Neja, da kuma Alhaji Liman Sulaiman, Deji Adeyanju, Zainab Suleiman Okino da Dr. George Agbakahi.