Majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani kan zargin cewa wasu ministocin gwamnatinsa sun biya kuɗi domin samun muƙamansu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, majalisar ta ce zargin da ake dangantawa da kakakin yaƙin neman zaɓen Tinubu, Alwan Hassan, ya haifar da tambayoyi kan yadda aka zaɓi ministocin gwamnatin tarayya.
ADC ta ce Hassan ya yi wannan ikirari ne a wani shirin talabijin kai tsaye, inda aka ruwaito shi yana cewa wasu ministoci sun biya kuɗi domin samun muƙamansu, kuma yanzu sun fi mayar da hankali wajen dawo da kuɗin da suka kashe kafin su mayar da hankali kan ayyukan gwamnati.
- An bar fursunoni 50 a ɗaki mai cunkoso duk da kukan neman agaji — rahoto
- Tinubu ya nemi Majalisa ta faɗaɗa yarjejeniyar musayar fursunoni zuwa ƙasashen wajen Commonwealth
To sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen ministocin ko adadin kuɗin da ake zargin an biya ba.
Majalisar ta buƙaci Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan ko yana da masaniya game da zargin, ko an fara bincike, da kuma matakan da gwamnatinsa za ta ɗauka.
Ta kuma nemi Hassan ya bayyana sunayen waɗanda ake zargi da hannu, adadin kuɗin da aka biya da kuma waɗanda suka karɓa.
Bugu da ƙari, ADC ta buƙaci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, ciki har da EFCC da ICPC, su gudanar da bincike mai zaman kansa, sannan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi bincike a bainar jama’a.
Ƙungiyar ta jaddada cewa zargin bai maye gurbin buƙatar hujja da bin tsarin doka ba, yayin da take kira ga ’yan Najeriya su binciki ayyuka da manufofin shugabannin siyasa gabanin zaɓen 2027.