Wani kwamitin bincike kan mutuwar fursunoni 33 a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Minna, Jihar Neja, ya ba da shawarar sake fasalin shugabancin hukumar da inganta tsarin kula da waɗanda ake tsare da su domin hana sake faruwar irin wannan lamari.
Rahoton ya bukaci a gina ingantattun wuraren tsare mutane a dukkan kwamandojin NSCDC, tare da sanya kyamarorin CCTV a wuraren da ake tsare da fursunoni domin ƙarfafa sa ido kan yadda ake kula da su.
- Kwamitin bincike ya ce an gudanar da samamen haƙar ma’adinai a Neja ba tare da cikakken tsari ba
- ’Yan sanda sun ƙwace motar da ke ɗauke da lambar Fadar Shugaban Ƙasa da ake zargin ta bogi a Abuja
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS, ya kuma ba da shawarar kafa wani tsarin sa ido mai zaman kansa kan wuraren tsare mutane, tare da inganta horar da jami’ai kan haƙƙin ɗan Adam da hanyoyin kula da fursunoni.
Bugu da ƙari, rahoton ya nuna bukatar ƙarfafa hanyoyin ba da agajin gaggawa na lafiya, inganta tattara bayanan sirri da kai rahoton barazana, da samar da isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan hukumar.
Kwamitin ya ce gazawar shugabanci, rashin ingantattun wuraren tsare mutane da ƙarancin sa ido na daga cikin matsalolin da suka taimaka wajen faruwar mutuwar fursunonin.
Ya bukaci a aiwatar da gyare-gyare masu zurfi domin tabbatar da kare rayuka da haƙƙin mutanen da ke hannun hukumar.