Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani direba tare da ƙwace motar Toyota Corolla kirar baƙi da ke ɗauke da lambar rajistar Fadar Shugaban Ƙasa mai lamba M01-997 FG, bisa zargin cewa akwai rashin tabbas kan sahihancin lambar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar 27 ga Oktoba, 2026, ta ce jami’an ’yan sanda sun tare motar ne da misalin ƙarfe 2:35 na rana a ranar 26 ga Oktoba, bayan samun sahihan bayanan sirri.
- Tinubu ba shi da shirin ɗaga Birnin Tarayya daga Abuja zuwa Legas – A4A
- INEC ta ce tana binciken hotunan AI da aka gano a rajistar masu zaɓe
Sanarwar ta ce an kai motar da direban zuwa hedikwatar rundunar ’yan sandan FCT domin gudanar da bincike na musamman kan lamarin.
A yayin binciken farko, rundunar ta ce direban bai bayar da gamsasshen bayani kan inda ya samo lambar rajistar ba.
’Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike domin gano yadda aka ba da lambar, mai motar da kuma sahihancin takardun rajistar.
Rundunar ta buƙaci mazauna Abuja su kasance masu bin doka tare da kai rahoton duk wani mutum ko aiki da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.