Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce rundunar za ta ƙara sayen kayan aikin tsaro da kamfanonin cikin gida ke ƙerawa domin rage dogaro da ƙasashen waje da kuma ƙarfafa tsaron ƙasa.

Ya bayyana hakan ne ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar kamfanin PROFORCE Group a Jihar Ogun, inda ya jaddada muhimmancin ƙera motocin yaƙi masu sulke da kayan kariya a cikin gida domin biyan buƙatun sojoji.

Janar Shaibu ya yaba wa kamfanin bisa ƙirƙire-ƙirƙirensa da gudummawar da yake bayarwa wajen ƙera kayan tsaro a Najeriya.

Ya ce zuba jari a wannan fanni zai rage dogaro da masu samar da kayayyaki daga ƙasashen waje, tare da inganta samun kayan aiki da kuma taimaka wa sojoji wajen tunkarar barazanar tsaro.

Ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da tallafa wa shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa masana’antun cikin gida da ƙarfafa ƙera kayan aikin tsaro a Najeriya.

A cewarsa, ingantacciyar masana’antar tsaro ta cikin gida na da muhimmanci wajen samar da fasaha, musayar ilimi da bunƙasa ƙarfin aikin sojoji na dogon lokaci.

A nasa ɓangaren, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na PROFORCE Group, Ade Ogundeyin, ya gode wa hafsan sojojin bisa ziyarar, tare da tabbatar da cewa kamfanin zai ci gaba da samar da kayan aikin tsaro masu inganci waɗanda za su dace da buƙatun rundunar sojojin ƙasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *