Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya yi bankwana da ɗalibai 65 da suka tashi zuwa ƙasar China domin karatun digiri na biyu da na uku a fannin noma da sauran fannoni masu alaƙa da shi.

Ɗaliban sun haɗa da masu karatun digiri na biyu (Master’s) guda 50 da masu digiri na uku (PhD) guda 15.

A cewar gwamnan, masu karatun digiri na biyu za su shafe shekaru uku, yayin da masu digiri na uku za su shafe shekaru biyar suna samun ƙwarewa a fannonin da suka shafi bunƙasa aikin noma a Jigawa.

Namadi ya ce tallafa wa ɗaliban wani ɓangare ne na ƙoƙarin zuba jari a fannin bincike, fasaha da bunƙasa ƙwararrun ma’aikata domin magance matsalolin da manoma ke fuskanta.

Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙarfafa cibiyoyin binciken noma da nazarin muhimman amfanin gona kamar su alkama, da shinkafa.

Gwamnan ya buƙaci ɗaliban da su mai da hankali kan karatunsu, su mutunta dokoki da al’adun ƙasar China, tare da yin amfani da damar da suka samu yadda ya kamata.

Ya kuma tunatar da su cewa kuɗaɗen da aka ɗauki nauyin karatunsu da su na jama’a ne, don haka ana sa ran za su dawo su yi amfani da ilimin da suka samu wajen yi wa al’ummar Jigawa hidima.

Namadi ya taya ɗaliban da iyalansu murna, tare da yi musu fatan nasara da tafiya lafiya. Ya ce yana sa ran dawowarsu bayan kammala karatu domin su ba da gudummawa wajen sauya fasalin aikin noma a jihar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *