Majalisar Dattawan Najeriya ta karanta a karon farko kudirin dokar kafa Jami’ar Nazarin Ayyukan Majalisa ta Yammacin Afirka ta shekarar 2026, wanda ke neman mayar da Cibiyar Nazarin Ayyukan Majalisa da Dimokuraɗiyya (NILDS) zuwa cikakkiyar jami’a.
Kudirin mai lamba SB.1087, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya gabatarwa, na da nufin bunƙasa ilimin ayyukan majalisa, shugabanci bisa tsarin dimokuraɗiyya, bincike da ƙarfafa cibiyoyin gwamnati.
- ADC ta ce jadawalin yaƙin neman zaɓen da ke yawo ba nata ba ne
- Atiku ya yi alƙawarin rage haraji ga sabbin kamfanoni, idan ya ci zaben 2027
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ingancin dimokuraɗiyya na da alaƙa da ƙwarewar waɗanda aka damƙa wa alhakin yin dokoki, sa ido kan ayyukan gwamnati da wakiltar al’umma.
Ya bayyana cewa kafa jami’ar na iya ba da damar samar da cibiyar ƙwarewa a matakin yankin Yammacin Afirka, inda ’yan majalisu da sauran jami’an gwamnati za su samu ilimi da ƙwarewar da za su taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da haɗin gwiwar ƙasashen yankin.
Akpabio ya jaddada cewa kudirin yana matakin farko na tsarin majalisa, amma ya ce Majalisar Dattawa ta 10 za ta ci gaba da tallafa wa dokokin da za su ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, inganta shugabanci nagari da kuma sanya Najeriya ta zama cibiyar ƙwarewa a fannin jagorancin dimokuraɗiyya.