Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanar da cewa mataimakin manajan daraktansa, Bo Li, zai bar muƙaminsa a ranar 30 ga Nuwamba, 2026, bayan kammala wa’adinsa, yayin da aka gabatar da Min Liao, mataimakin ministan kuɗin China, domin maye gurbinsa daga 1 ga Disamba.
Manajan daraktar IMF, Kristalina Georgieva, ce ta bayyana hakan a cikin sanarwar da ta fitar a ranar 28 ga Oktoba, 2026, a Washington, DC.
Ta yaba da gudummawar Bo Li tun bayan shigarsa hukumar a watan Agustan 2021, musamman wajen tafiyar da ayyukan asusun a lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar ƙalubale.
- Majalisar Dattawa ta fara nazarin kudirin kafa Jami’ar Nazarin Ayyukan Majalisa ta Yammacin Afirka
- Atiku ya nemi Tinubu ya riƙa wallafa hotuna da bidiyo daga Makka kullum
A muƙaminsa, Bo Li ya kula da ayyukan IMF da suka shafi ƙasashe mambobi kusan 90, tare da jagorantar wasu tsare-tsare da suka haɗa da kula da haɗarin kasuwanci, inganta tsarin bayanai, kuɗin dijital, biyan kuɗi tsakanin ƙasashe da dokokin stablecoin.
Haka kuma, ya taimaka wajen tsara ayyukan hukumar kan basussukan ƙasashe, shugabanci nagari, cin hanci da rashawa da kuma amfani da fasahar basirar wucin gadi.
Georgieva ta bayyana Min Liao a matsayin gogaggen masani kan harkokin kuɗi da tattalin arziki, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a bankuna, harkokin tsara dokokin kuɗi da manufofin tattalin arziki.
Ta ce gogewarsa a haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashe za ta taimaka wa IMF da ƙasashe mambobinta.

Liao ya kasance mataimakin ministan kuɗin China tun watan Mayun 2018, kuma mamba ne a kwamitin tsara manufofin kuɗi tun shekarar 2023.
A baya, ya yi aiki a Bankin Jama’ar China, China Everbright Group, Bankin China da Hukumar Kula da Bankuna ta China, inda ya riƙe muƙamai daban-daban.
Liao ya yi digiri na biyu a fannin tattalin arziki a Jami’ar Peking, sannan ya samu digirin MBA a Jami’ar Cambridge.
IMF ta bayyana naɗinsa a matsayin shawarar da aka gabatar, wadda za ta fara aiki a ranar 1 ga Disamba, 2026, idan an amince da ita.