Dakarun Operation Hadin Kai sun ce sun kashe ’yan ta’adda 44 tare da jikkata wasu 24 a hare-haren da suka kai kan maboyarsu a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da mukaddashin jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar 28 ga Oktoba, 2026, ya ce dakarun sun kai hare-haren ne a wurare daban-daban na ƙaramar hukumar Kukawa da ke Borno, bayan samun bayanan sirri a ranar 26 ga Oktoba.

Sanarwar ta ce tantance sakamakon hare-haren ya nuna cewa an kashe ’yan ta’adda 28, yayin da wasu shida suka samu raunuka.

A wani samame da rundunar sojojin ruwa ta kai a yankin Tafkin Chadi, an kashe wasu ’yan ta’adda takwas tare da jikkata 10 a ranar 28 ga Oktoba.

Haka kuma, rundunar ta ce wani harin sama ya tarwatsa shirin wasu ’yan ta’adda na dasa bama-baman da ake sarrafawa da hannu, inda aka kashe mutum takwas tare da lalata motarsu, babura da kayan aikin bama-baman.

Rundunar ta bayyana cewa hare-haren na daga cikin ƙoƙarin raunana ƙarfin ’yan ta’adda da hana su gudanar da ayyukansu, tare da kare al’ummomin yankin Arewa maso Gabas.

Ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *