Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce ƙasar na bukatar manyan ayyukan more rayuwa domin cimma burinta na gina tattalin arzikin da ya kai dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.

Ya bayyana hakan ne yayin kare shirin rancen kuɗin da gwamnatinsa ke karɓa daga ƙasashen waje da cibiyoyin kuɗi, yana mai cewa abin dubawa shi ne amfanin da za a samu daga kuɗin da aka aro.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 29 ga Oktoba, 2026, Tinubu ya ambaci manyan ayyuka da suka haɗa da babbar hanyar Lagos–Calabar, Sokoto–Badagry da Trans-Sahara, da kuma gyaran lantarki da zamanantar da manyan tashoshin jiragen ruwa na Legas.

Ya ce ayyukan za su haɗa yankunan tattalin arziki, rage kuɗin jigilar kaya, buɗe damar bunƙasa noma da masana’antu, tare da jawo masu zuba jari.

Gwamnatin ta ƙiyasta cewa hanyar Lagos–Calabar kaɗai na iya samar da ayyukan yi kai tsaye kusan 100,000, da wasu sama da 150,000 a fannonin sufuri da samar da kayayyakin gini.

Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin 100 a zangon biyu na shekarar 2026, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 14.63 cikin 100 a watan Satumba.

Ya kuma bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta kai dala biliyan 55.1 a ranar 9 ga Oktoba, yana danganta ci gaban da sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara tun 2023.

Shugaban ya jaddada cewa nasarar shirin tattalin arzikin ba za ta ta’allaka da karɓar rance kawai ba, sai an kammala ayyuka, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.

Ya ce gwamnatinsa za ta kuma mayar da hankali kan rage tsadar abinci da makamashi, kiyaye tsarin kasafin kuɗi da tallafa wa iyalai masu buƙata.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *